Ya Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari dubun gaisuwa da jinjina ta musamman zuwa gare ka, ina fata wannan shawarar tawa za ta same ka cikin koshin lafiya. Bayan haka ina amfani da wannan damar domin in kara yaba maka a kan wasu abubuwan da kake yi na alheri a cikin kasar nan. Ko shakka babu, babu abin da za mu ce maka sai godiya da fatan alheri.
Ya Shugaban kasa Baba Buhari! Sai dai akwai wasu ’yan matsaloli masu zuwa suna dawowa, musamman a daidai wannan lokaci mai wahalar gaske da kowane dan kasa yake ji a jikinsa, ta wasu bangarori. Hausawa suna cewa ‘Domin tuwon gobe ake wanke tukunya’ a daidai wannan lokaci da ake tunkaro babban zaben kasar nan kuma abubuwa suka dada dagulewa na tsadar rayuwa a cikin al’umma, akwai bukatar ka waiwayo don saukaka wa talakan kasar nan.
Ya Shugaba Buhari duk da mun san cewa abubuwa sun yi maka yawa haka kuma hannu daya ba ya daukar jinka amma duk da haka ya kamata a kara kaimi domin ganin an fitar da Najeriya zuwa ga tudun mun-tsira. Mun san cewa a cikin gwamnatinka akwai ’yan hana ruwa gudu wadanda suke son yin amfani da wata dama ta kashin kansu, domin ganin ka gaza wajen kula da talakawanka, amma har yanzu mun yi imani cewa kana iyakacin kokarinka domin ganin cewa talakan kasar nan ya samu farfadowa daga mugunyar doguwar sumar da ya yi a gwamnatin da ta shuɗe, amma kuma hakan kada ya tsorata ka wajen tashi tsaye ka yi tsayin daka domin kwato wa talaka hakkinsa kamar yadda ka lashi takobin yin haka tun farko.
Ya Shugaba Buhari har yanzu muna tare da kai mu talakawan kasar nan, saboda haka muna son ka kara kaimi domin ganin kasar nan ta ci gaba ta kowane fanni.
Ko shakka babu kifi na ganin mai jar koma, na fadi haka ne ganin masu yi maka zagon kasa a cikin mulkinka wadanda insha Allahu ba za su samu nasara ba.
Ya Mai girma Shugaba kasa Buhari yana da kyau ka nemi shawarar tsofafafin shugabannin kasar nan wadanda ka tabbatar ba za su ba ka shawarar banza ba, domin ganin ka ciyar da kasar nan gaba. A karshe ina yin addu’a da fatan alheri ga kasarmu da Shugabanmu Muhammadu Buhari. Allah Ya yi masa kariya Ya sa ka gama mulkinka cikin koshin lafiya.
Mai Apple ɗan kishin marasa galihu, kuma dan kungiyar Muryar Talaka ta kasa reshen Jihar Zamfara ya rubuto makalarsa ce daga Gusau, 08133376020/08086679022