✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budaddiyar wasika ga Sarkin Musulmi

Ni ba malami ba ne, kuma ba masanin Shari’a ba ne ko tarihin addinin Musulunci, amma a matsayina na mai suna Usman Adamu da aka…

Ni ba malami ba ne, kuma ba masanin Shari’a ba ne ko tarihin addinin Musulunci, amma a matsayina na mai suna Usman Adamu da aka fi sani na da Doya Amsin. Ina zama a garin Agyaragu ne a Jihar Nasarawa. Kuma  ina so in yi kira ne ga Shugaban Majalisar Sarakunan Musulmi, Mai martaba Sarkin Musulmi na Saukoto, wanda ke daya daga cikin wadanda ke jagoranci al’umma a nahiyar Afirka.
A takaice shekaru na sun kai 60 a duniya, kuma na tashi na ga yadda malamai a Najeriya suke wa’azi daban-daban. Kowa da irin fahimtar da Allah ya yi masa. Saboda haka kiran da zan yi ga Sarkin Musulmi, shi ne, kungiyoyin Musulunci mabambanta da ke kasar nan baki daya ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira a garesu da su yi zama da shugabanninsu, saboda wadannan abubuwa da suke tunkararmu na rikita-rikita, da kuma zabe mai zuwa na shekarar 2015. Wannan nauyi da Allah ya aza masa, ko in ce ya gada. Kuma da alama tun daga zuwansa, kyama da son kai da ke tsakanin kungiyoyin addinin Musulunci a kasar nan, an samu sauki sosai, musamman wadannan kungiyoyi da kowannensu ke kira abi Allah, abi manzonSa.
To, mu mabiya da yawa akwai wasu abubuwa da ba mu fahimta ba. Kowa zai zo ya ce Allah ya ce kaza, aAnnabi ya ce kaza, amma idan ka ga mutane biyu suna husuma akan addinin Musulunci, abin da ya kamata ka lura shi ne addinin nan fa na Allah ne, kuma Allah ya ce addini a wurinSa shi ne, musulunci. Ke nan wadannan Musulmi da suke ta fadace-fadacen nan an kuma kafa kungiyoyin nan a karshe fa mu sani cewa kowa zai koma ga manzon Allah (S.A.W) ne.
Masu yi na gaskiya Allah ya sansu, masu fakewa da ma’aiki don su cuci musulmi, dukkansu mu da ba mu yi karatu ba, amma mun fahimci inda gaskiya ta ke. Shi yasa wannan damar da na samu nake kira ga Mai martaba Sarkin musulmai da ya gayyaci wadannan kungiyoyin da suka hada da Jama’atil Nasaral Islam da Jama’atu Izalatir Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da Fitiyanu Islam da kuma kadiriya, wadanda kowa cikinsu ke yin kira akan abin da ya fahimta. Za ka ga suna karanta hadisai, za ka ga suna karanta Alkur’ani, kowa yana bada hujja kamar yadda ya fahimta. To, sai ya kasance ana samun rarrabuwa a tsakaninsu, to rarrabuwan ce da kowa na ganin shi ne akan gaskiya muke so su gane cewa addinin nan fa daya ne, duk inda ka tafi a duniya. Haka ma Alkur’ani daya ne, sai dai hadisai da muke ji malamai suna bambantawa, akwai masu inganci, akwai kuma masu rauni. Duk wadannan in ba malaman da suke bincike ba, ba a sani ba. Za ka ga kowa yana cewa shi ya dogara ga wane, wancan yana shi ya dogara ga wane. Na tabbata hakan ke jawo rarrabuwa a tsakaninsu. To, shi ne nake so Mai martaba Sarkin musulmai dan Allah dan annabi dakanmu zamu mutu.
Da malami da wanda ba malami ba, duk za mu koma ga Allah, a tara shugabannin wadannan kungiyoyi a tambayesu, mene ne ya kawo wadannan rarrabuwa ko in ce bambance-bambancen nan. Ka ga wajen sallah ba a rabu ba, wajen tauhidi ba a rabu ba, haka ma wajen zakka da wajen amsa sallawatinnan da Kalmar shahada da dai sauransu duka daya ne. Idan haka ne to me ke kawo rarrabuwa a tsakanin kungiyoyin addinin Musuluncin nan? Duk da cewa harshen Larabci a nan Najeriya zan iya cewa a kashi 99 cikin 100 yawanci ba sa jin sa.
An ce akwai wasu litattafan dariku da sauransu da suka yi bayyane, wanda idan aka bi fasararsu ma da yawan mu ba za mu gane ma’anarsu ba. Shi ya sa nake so Sarkin Musulmi ya kira kowa ya zo a kuma tara mutane a Cibiyar Arewa da ke Kaduna, a zauna a gano irin kiran da ake yi kan mene ne bambancin wane da wane.
Duk abubuwa da aka ce a yi koyi da Ma’aiki manzon Allah (S.A.W), dukka darikunnan kuma litattafe da wasu suka ce wasu dariku suna dasu wanda akwai mai kyau a ciki akwai kuma wanda watakilla kuskure ne akayi. To, a bayyana wa jama’a. A kasar Macca dai ai kowa yasan addinin musulunci ta gun ne. kuma duk musulmin duniya yanason zuwa gun. Kuma sai ya kasance idan an je gun bama ganin wani banbanci na addinin musulunci gun wadanda suka tafin. Sabodahaka sai a tambaya me ake yi anan Afirka da kuma nan Najeriya da ba ayinsa a can Macca inda tushin musulunci yake. Sai kuma mu duba me Manzon Allah (S.A.W) ya yi da yake raye, kuma labarin da ya bayar mene ne ma’anarsa? To, idan an fahimci mutane irin wadannan abubuwa ba shakka za a samu hadin kan musulmai a kasar nan da ma Afirka baki daya.
Irin kalubalan da ya kamata mu tunkare shi ke nan, musamman mu a nan Arewa. Tunda ko Kirista da Arewa yasan a cikin jihohi 19 da ke cikin Arewan nan idan aka hada Musulunci ne ya yi rinjaye. Haka ma a can kasar Yarbawa in an hada su gaba dayansu da Musulmi da Kiristoci an san musulmai ne ke da rinjaye. Yau a ce boko haram gobe a ce wane, a dai dauki abin da ba ka sani ba a manna maka, a tsakaninmu musulmi ke nan fa hakan ke faruwa, don dai a hallaka ka, ko a dakushe ka. Shi yasa nake kira ga Mai martaba Sarkin Musulmi cewa ni talaka ne cikakke, wallahi ban san komai ba. Amma yadda muke shiga wurare muna jin wa’azi, muna tsintar wasu abubuwa, hade da kishin kasar mu Najeriya, musamman Arewa, shi ya sa nake kira ga Mai martaba Sarkin Musulmi da ya yi wa Allah, ya yi amfani da wadannan hanyoyi da na bayyana. Kuma na tabbata da yardan Allah idan har ya bi shawarar za a shawo kan wadannan miyagun kalubale da musulmin kasar nan ke fuskanta.
Doya Amsin ya rubuto ne daga Agyaragu, Jihar Nasarawa.