✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BUA ya rage farashin siminti zuwa N3,500 duk buhu

BUA ya sauko da farashin buhun siminiti daga N5,000 zuwa N3,500.

Kamfanin Siminti na BUA, ya sanar da cewa daga gobe Litinin 2 ga watan Oktoba farashin buhun siminti zai koma naira dubu uku da dari biyar (N3,500).

A cikin sanarwar da ya fitar a Yammacin wannan Lahadin, kamfanin BUA ya ce sabon farashin zai maye wanda a baya ake bai wa dilallan buhun simintin kan naira 4,650, su kuma sayar da shi a kasuwa kan naira dubu 5,000.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin rage farashin ne a sakamakon sauki da ya samu wajen siyan kayayyakin da ake sarrafa siminitin da kuma kammala wasu manyan ayyukan kamfanin da ke haifar da tsadar simintin.

A cewar kamfanin, wannan wani mataki ne na ganin ‘yan Najeriya sun samu damar yin gine-gine cikin sauki da kuma saukaka farashin kayan gine-ginen.

Kamfanin ya ce da zarar an kammala aikin sabbin layukan da kamfanin ke yi a halin yanzu, zuwa sabuwar shekara, kamfanin zai sake duba yiyuwar rage farashin.

A cewar sanarwar: “Dangane da bayanin da muka fitar a baya na niyyar da muke da shi na rage farashin siminti da zarar mun kammala bude sabbin layukanmu a karshen shekara, domin bunkasa kayan gini da sashin gine-gine.

“A cikin yunkurinmu na rage farashin kayayyakinmu da sake nazartar ayyukanmu lokaci zuwa lokaci, hukumar gudanarwa ta kamfanin BUA na sanar da abokan huldarta da masu ruwa da tsaki hadi da sauran al’umma cewa daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023, mun cimma matsayar rage farashin.

“A kan hakan, daga yanzu za a sayar da buhun simintin BUA ne a kan naira 3,500 domin ‘yan Najeriya su fara cin moriyar farashin kafin mu kammala tsare-tsarenmu.”

A cewar sanarwar, wani karin tagomashi ma shi ne, dukkanin wadanda suka yi odar sayo simintin a kan tsohon farashi a halin yanzu, za a duba a mayar da shi zuwa naira 3,500 a bisa tsarin sabon farashin da zai fara aiki daga ranar 2 ga Oktoba.

Kamfanin ya shawarci dillalansa da su tabbatar jama’a sun amfana da wannan sabon farashin kuma kamfanin zai sanya ido wajen ganin an bi umarnin amfani da sabon farashin ba tare da wata tangarda ba.

Ana iya tuna cewa, a makonnin da suka gabata ne bayan wata ziyara da kai wa Shugaban Kasa Bola Tinubu, shugaban rukunin kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya sanar da cewa, kamfanin ya shirya tsaf domin rage farashin siminti a Najeriya zuwa N3,500 ko ma kasa da haka.