Manyan attajiran Kano Aliko Dangote da Abdussamad Rabi’u na musayar yawu da zargin yi wa juna zagon kasa a harkokin kasuwancinsu.
Wannan dai na zuwa yayin da rukunin Kamfanonin Dangote da ke Najeriya ya musanta zargin cewar ya sanya kansa cikin haramcaciyar musayar kudaden waje, inda ya gargadi masu yada irin wannan zargin cewar ya na yiwa kasa zagon kasa, da su kaucewa yin haka.
- Sojoji sun kai hari kusa da fadar Shugaban Kasar Guinea
- Zaɓen Kano: Ranar Litinin Kotun Daukaka Kara Za Ta Saurari Karar Abba
Kamfanin ya gabatar da wannan gargadi ne sakamakon wasu rahotannin da aka wallafa a kafofin intanet dake zargin cewar shugaban kwamiti na musamman da shugaban Najeriya ya kafa Jim Obazee domin binciken ayyukan Babban Bankin Najeriya a karkashin jagorancin Godwin Emefiele na gudanar da bincike a kan sa saboda hannu wajen wannan badakalar da kuma halarta kudaden harum.
Sanarwar da kamfanin ya gabatar ta ce, Dangote ya bayyana rahotanin a matsayin masu tsauri, yayin da ya zargi abokin adawarsa, wato kamfanin BUA da hannu a ciki dumu dumu.
Dangote yace tun daga shekarar 2016 aka fara yada irin wadannan labarai na kanzon kurege a jaridun BusinessDay da Leadership, inda yace sun sake farfado da su ne yanzu domin gabatar da su kamar wasu sabbin labarai.
Kamfanin yace abin takaici ne yadda a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2016, Jaridun BusinessDay da Leadership suka wallafa rahotan cewar Kamfanin Dangote ya karkata Dala biliyan 3 na kudaden waje zuwa wasu kamfanoninsa dake wajen Najeriya, matakin dake da nasaba da halarta kudaden haramun.
Dangote ya ce wancan rahotan da aka yi a shekarar 2016 shine kuma aka sake wallafa shi a yanzu da sunan wani Ahmed Fahad, a matsayin korafin da aka gabatarwa shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Jim Obazee, shugaban kwamitin bincike na musamman dake gudanar da bincike a kan ayyukan Babban Bankin Najeriya.
Kamfanin ya ce abin takaici shine yadda wasu kafofin intanet suka dinga daukar labarin suna wallafa shi da zummar bata masa suna.
Dangote ya ce yunkurin wadanda suka kitsa wannan labari na kawar da hankalin jama’a da kuma farfado da tsohon labarin abin takaici ne, ganin yadda wadancan jaridu guda 2 da suka wallafa shi a shekarar 2016 suka fito fili suka kuma nemi gafarar shugabannin kamfanin Dangoten da kuma janye labaran da suka yi a kai baki daya.
Kamfanin ya ce Jaridun BusinessDay da Leadership sun tabbatar da cewar kamfanin BUA ne ya dauki nauyin wallafa rahotannin.
Dangote ya ce yana samo kudaden waje domin gudanar da ayyukansa ne ta hanyoyin bankuna kamar yadda dokokin CBN suka tanada, kuma suna gabatar da takardun da suka dace wajen samun kudaden sayen kayayyakin aiki da kuma kafa kamfanonin su ciki harda na siminti.
Kamfanin ya ce an kuma bayyana karara yadda aka gudanar da hada hadar kudaden da kuma lokacin da za’a biya basussukan da aka karba kamar yadda ka’idodin duniya suka tanada.
Dangote yace babu wani lokaci da suka saba ka’ida wajen gudanar da harkokin su na karbar kudade daga bankuna, ko kulla harkokin kasuwanci ko kwangila ko kuma biyan kudaden da suka dace.
Kamfanin ya ce wannan ta sa manyan jami’an gwamnatin Najeriya tare da shugabannin bankuna, tare da na manyan kamfanoni da ma shugabannin kasashen waje halartar bukukuwan kaddamar da kamfanonin sa.
Dangote yace kudaden da ya karkata zuwa fadada ayyukan da yake yi a kasashen Afirka halartattu ne da suka fito daga masu zuba jari a wadannan kasashe, yayin da shigo da Dala miliyan 576 zuwa Najeriya da yayi ya taimaka wajen daidaita kasuwannin kudaden ketare.
A karshe kamfanin ya sake jaddada cewar yana fadada ayyukan kamfanoninsa ne ta hanyar samun kudaden ketare ta bankuna kamar yadda dokokin CBN suka tanada, kuma lokaci zuwa lokaci ya na gabatar da rahoto ga bankunan domin mika su ga Babban Bankin Najeriya.
Tun shekaru 32 da suka gabata Dangote yake mana zagon kasa — BUA
Kamfanin BUA ya mayar da martani a kan zargin bata sunan da ya ce Aliko Dangote ya masa ta kafofin yada labarai, inda ya musanta zarge zargen da kuma karin haske a kan takun sakar da ke tsakanin su tun daga shekarar 1991.
Sanarwar da kamfanin BUA ya gabatar ta ce, sun fara samun matsala da Dangote ne tun daga watan Agustan shekarar 1991, lokacin da suka dauki aniyar bunkasa aikin samar da sikari wanda a lokacin yayi karanci a Najeriya.
Kamfanin BUA ya ce a wannan lokacin ya zama daya daga cikin wadanda suka samu lasisin samar da sikarin, abinda ya sa Aliko Dangote ya tinkare su domin sayen sikarin daga wurin su, amma basu san cewar yana shirya musu zagon kasa ba ne.
Sanarwar tace bayan sun kulla ciniki, Dangote ya basu cakin kudi na bankin Societe Generale na bogi, amma da suka je karbar kudi sai suka tarar da babu a bankin, abinda ya kai ga maka su a kotu da kuma rufe kadarorin da suka mallaka sakamakon zagon kasan da suka ce Dangoten ya musu.
BUA ya ce wannan ta sa hukumomi suka rufe musu asusun ajiyar bankun su na watanni 3, tare da rufe wuraren ajiye kadarorin su da kuma gwada karfin imanin su.
Kamfanin ya ce bayan wancan takaddamar da suka tsallake, bayan yan shekaru sun bukaci bude kamfanin sarrafa sikari domin inganta harkokin su a Lagos, saboda haka suka tintibi wani da ake kira Usman Dantata kafin Allah Ya masa rasuwa, wanda kawu ne ga Aliko Dangote, inda suka karbi hayar filinsa a tashar ruwan Tincan.
Bayan sun rattaba hannu a kan yarjejeniya tare da sanin hukumar dake kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya ta NPA da kuma biyan hakkokin da suka rataya a kan su, Dangote ya je wurin shugaban kasa na wancan lokaci Olusegun Obasanjo domin gabatar da korafi a kai.
BUA ya ce Obasanjo ya bada umurni soke lasisin filin da kuma mika mallakar sa ga Dangote, matakin da ya kaiga Kawunsa (Usman Dantata) yayi asarar filin, yayin da aka baiwa BUA umarnin barin filin cikin sa’oi 24, daga bisani sanda suka kwashe shekara guda kafin samun wani filin na daban.
Kamfanin ya ce filin da ya mallaka domin kafa wurin sarrafa sikarin sa a Lagos a yau ya fito ne daga mahaifin shugaban su, wanda ya mallaka masa kyauta, abinda ya kai ga daga darajar su ta zama kamfani mafi girma dake sarrafa sikari a Yankin Afirka ta Yamma.
BUA ya ce daga nan kamfanonin su, sun ci gaba da habaka duk da gadar zaren da ake shirya musu suna tsallakewa.
Kamfanin ya kuma kara da cewar a shekarar 2007 lokacin mulkin shugaba Umaru Musa Yar’Adua da ake bukatar bunkasa harkokin samar da siminiti da kuma kawar da mamayar da wasu suka yi a bangaren, an baiwa wasu kamfanoni guda 6 lasisi ciki harda BUA, amma kokarin su na samun inda zasu dinga sauke siminiti a Lagos ya fuskanci matsala, dalilin da ya sa suka karkata zuwa Fatakwal.
BUA ya ce ba karamar adawa suka fuskanta ba har sanda shugaba Yar’Adua ya bada umarni ga ministan sufuri da shugaban hukumar NPA cewar ya zama wajibi a basu damar bada gudumawa a wannan bangaren.
Kamfanin yace ya yin da ake wannan sai wani mataimakin shugaban hukumar shigi da fice da ake kira Orwell Brown wanda wansa ke aiki da Dangote ya kaddamar da yunkurin korar ma’aikatansa ‘yan kasashen Asia, abinda ya tada hankalin su da kuma tilasta su tintibar mai baiwa shugaban kasa shawara a kan tattalin arzikin kasa, Tanimu Yakubu wanda nan take ya kira shugaban hukumar ta kasa dan dakatar da korar ma’aikatan wadanda aka shirya sanya su a jirgin Emirates domin tilasta musu barin Najeriya.
BUA ya ce daga bisani Brown ya amsa tuhumar da Minista ya masa, abinda ya sa aka kore shi daga aiki.
Kamfanin ya kuma tabo irin adawar da ya fuskanta wajen kafa kamfaninsa na siminiti da ke Edo da kuma irin gudumawar da shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Obaseki suka bayar wajen ganin ba’a hana su aikin ba, tare da matsalar da suka fuskanta wajen kafa kamfanin sarrafa sikarin su dake Fatakwal.
BUA ya ce duk da wadannan matsaloli da yayi ta fuskanta, gwuiwar sa bata yi sanyi ba a kokarinsa na kawo sauki ga kasa da kuma gudanar da harkokin kasuwanci ta hanyar da doka ta tanada.