✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kashe mutum 13 a gidan rawa a Sfaniya

Ana fargabar sauran ginin gidan rawar da ke tsaye zai iya ruftawa a kowane lokaci.

Wata gobara da tashi a gidan rawa da ke yankin Murcia na kasar Sfaniya ta yi sanadin mutuwar mutane 13, yayin da ake fargabar adadin ka iya karuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan da wutar ta kama kuma sai ginin ya rufta kan jama’ar da ke cikin gidan rawar.

Wutar wadda har yanzu babu tabbaci kan dalilin tashinta, ta ratso ne daga wani gidan rawar da babu kowa a cikin sa ta kuma shiga inda mutane ke tsaka da holewa.

Hukumar kashe gobara ta kasar ta ce har yanzu masu aikin ceto na ci gaba a laluben mutanen da baraguzan gine-gine suka danne.

Magajin Garin Murcia, Jose Ballesta ya shaida wa manema labarai cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiya agogon kasar, kuma nan take ta yi karfin da aka kasa shawo kanta cikin gaggawa.

Ballesta ya kuma ci gaba da cewa har kawo yanzu ana ci gaba da aikin neman mutane cikin baraguzan gine-gine, yayin da ake fargabar sauran ginin gidan rawar da ke tsaye zai iya ruftawa a kowanne lokaci.

Babban sufeton ‘yan sandan kasar Diego Seral ya ce gidan rawar da wutar ta tashi mai suna Fonda Club na cikin manyan gidajen rawa uku da kasar ke takama da su, kuma wanda ya fi kowanne tarihin tashin gobara.

Ya ce rushewar da ginin ya yi shi ne babban dalilin da ya sa har yanzu ba a kai ga tattara alkaluman mutanen da suka mutu ba, saboda akwai yakinin cewa za a iya samun mutanen a kasa.