Kamfanin BUA ya raba kyautar tan 150 na siminti da kuma Naira Miliyan 10 ga kowanne daga al’ummomin yankunan da yake gudanar da harkokinsa a Karamar Hukumar Wamakko ta Jihar Sakkwato.
Kamfanin ya ce ya gwangwajen al’ummomin da suka ci gajiyar kyautar ne domin saukaka musu wani bangare na rayuwa.
“Manufarmu ita ce taimakon al’ummomi da abin da za su gyara gidajensu da wuraren taro da kuma makabartu,” inji shi Manajan Daraktan kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Binji, a lokacin rabon kayan a Sakatariyar Karamar Hukumar a ranar Laraba.
Injiniya Binji wanda ya samu wakilincin Sada Suleiman ya ce kamfanin na daf ba bayar da tallafin karatu ga dalibai marasa karfi a jihohin Kebbi da Sakkwato da kuma Zamfara.
Tun da farko, Shugaban Karamar Hukumar Wamakko, Bello Haliru Gwiwa ya yaba wa kamfanin kan karamcin da yi wa jama’ar.
Da yake magana a madadin al’ummomin da suka amfana, Hakimin Wamakko, Alhaji Aliyu Barade Wamakko, ya ce kayan za su taimaka wajen rage wa mutanen da suka ci gadiya radadin da suke ciki.
Ya kuma yi alkawarin cewa za su yi amfani da tallafin yadda ya kamata.