kasar Brazil ta amince da ta yi wasan sada zumunta da Najeriya a matakin ’yan kasa da shekara 23 (U-23). Ana sa ran wasan zai gudana ne a ranar 23 ga wannan wata da muke ciki a filin wasa na Kleber Andrade da ke Brazil.
Brazil ta sanar da haka ne a wata takarda da ta rubutowa Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) a karshen makon jiya.
Brazil ta ce ta shirya wannan wasa na sada zumunci ne a kokarin tunkarar gasar Olamfik da za a yi a kasar a watan Agustan wannan shekara, inda Brazil da Najeriya na daga cikin kasashen da za su fafata a bangaren kwallon kafa yayin gasar.
Idan za a tuna a shekarar 1996 ce Najeriya ta fitar da Brazil a matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal) a gasar Olamfik da ta gudana a Atlanta na Amurka. Ana saura minti 15 a tashi wasan ne Najeriya ta fanshe ci 3-1 da Brazil ta yi mata, kuma bayan an kara lokaci ne Najeriya ta sake jefa kwallo a ragar Brazil da hakan ya sa ta fitar da ita a gasar.
A wasan karshe (fainal) Najeriya ta sake doke Ajantina da ci 2-1 da hakan ya sa ta lashe lambar zinare a bangaren kwallon kafa. Hakan ya sa ta zama kasar Afirka ta farko a tarihin gasar a wancan lokaci da ta taba kai wa wannan matsayi.
Tun lokacin ne Brazil take mamakin yadda Najeriya ta samu nasara a kanta duk da zaratan ’yan kwallon da take ji da su irin su Bebeto a wancan lokaci.
Masana harkar kwallo suna ganin Brazil ta shirya wannan wasa ne don tabbatar da sahihancin ’yan kwallonta kafin watan Agustan wannan shekara da za a fara gasar Olamfik a kasar.
Koci Samson Siasia ne zai jagoranci kungiyar a gasar ta Olamfik kuma ana sa ran zai gayyato zaratan ’yan kwallo irin su Kelechi Iheanacho da sauransu a wasan na sada zumunci.
Brazil za ta kece raini da Najeriya
kasar Brazil ta amince da ta yi wasan sada zumunta da Najeriya a matakin ’yan kasa da shekara 23 (U-23). Ana sa ran wasan zai…