An samu rahotanni da ke nuna akalla mutum uku ne suka mutu a kasar Sin a yayin da suke kallon gasar cin kofin duniya da yanzu haka ake bugawa a Brazil. Mutanen da suke rasun sun fito ne daga yankuna daban-daban a kasar Sin watau Chaina.
Rahoton ya nuna wani mutum dan kimanin shekara 39 da ya fito daga yankin Shanghai a kasar Sin ya rasu a ranar Lahadin da ta wuce bayan ya shafe kimanin dare uku a jere yana kallon gasar a akwatin talabijin dinsa ba tare da ya runtsa ba.
Rahoyton ya ce mutumin da ake kiransa da Zhou ya mutu ne bayan ya kamu da ciwon rashin gudanar jini a jiki da ake wa lakabi da Stroke. An ce ya kamu da ciwon ne a lokacin da yake kallon wasan kasashen Uruguay da na Costa Rica. Rahoton ya ce an shaidi mutumin yana fama da matsalar hawan jini a mafi yawan lokuta.
Haka kuma an ruwaito wani dan kimanin shekara 25 shi ma ya mutu a dakin da yake ajiye na’ura mai kwakwalwa a gidansa da misalin karfe bakwai na safe agogon Sin a ranar Asabr da ta gabata a wani gari da ke Gabashin Suzhou da ke yankin Jiangsu na kasar.
An samu mutumin ne a mace a gaban talabijin dinsa a lokacin da yake kallon wasa a tsakanin kasar Holand da Sifen, bayan da Holan ta lallasa Sifen da ci 5-1.
Likitocin da suka yi wa mamacin gwaji sun tabbatar mutuwarsa ba ta rasa nasaba rashin samun isasshen barci da kuma matsalar bugun zuciya watau heart attack.
Haka kuma an samu rahoton mutuwar wani tsohon dan kwallo a kasar Sin mai suna Li Mingkiang, dan kimanin shekara 51 saboda matsalar bugun zuciya a gidansa da ke Arewa maso Kudancin birnin Shenyang a ranar Asabar shi ma jim kadan bayan ya kalli wasa a tsakanin kasashen Sifen da Holand. Rahoton ya ce ana kyautata zaton gajiya da kuma rashin samun isasshen barci na daga cikin abubuwan da suka haddasa mutuwar mamacin. An ce mamacin bai runtsa ba a lokacin da ya kalli wasa a tsakanin kasashen Chile da Australiya a akwatin talabijin dinsa. Rahoton ya ce wani abokin Li ne ya sanar da jami’an tsaro halin da ya tsinci abokinsa a gidansa bayan ya fadi sumamme amma kafin a kai shi asibiti rai ya yi halinsa.
Likitoci dai suna gargadi ga magoya bayan kwallon kafa a ko’ina suke a duniya da su rika kokarin runtsawa don samun isasshen hutu kafin su raba dare wajen kallon gasar cin kofin duniya da yanzu haka ke gudana a Brazil