✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bournemouth ta casa Liverpool a wasan mako na 26 na Firimiyar Ingila

Bournemouth ta samu nasarar fita daga ukun karshe a teburin Firimiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth ta doke Liverpool da ci 1-0 a wasan mako na 26 na Gasar Firimiyar Ingila.

Hakan ya bai wa Bournemouth samun nasarar fita daga ukun karshe a kan teburin Firimiyar yayin da kuma ta hana Liverpool din shiga sahun hudun farko a kan teburin.

Liverpool ta yi rashin nasararsa ne bayan da ta doke Manchester United da ci 7-0 a makon da ya gabata, yayin da ita kuma Bournemouth ta fara wasan a cikin ukun karshe a teburin Premier.

Rashin tsare gida da kyau ne ya sa Philip Billing ya zura kwallo a ragar Liverpool daga tazarar yadi takwas.

Liverpool ta samu bugun Fenareti a wasan bayan da kwallon da Diogo Jota ya sanya wa kai ta taba hannun Adam Smith.

To sai dai Mohammed Salah – wanda ya zama dan wasan da ya fi ci wa Liverpool kwallo a gasar Firimiyar inda ya ci kwallo ta 129 a makon da ya gabata – ya barar da bugun fenaretin bayan da ya buga ta waje.

A halin yanzu dai Liverpool tana zaman ta hudu da maki 42 yayin da Bournemouth ke zaman ta 16 da maki 24 a kakar Firimiyar bana.