Rahotannin da muka samu daga Jihar Borno a safiyar Asabar na cewa dakarun sojin Najeriya sun yi dauki ba dadi da mayakan kunigyar ISWAP a yankin Askira/Uba na jihar.
Mataikamin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Injiya Abdullahi Musa Askira, wanda shi ke wakiltar yankin, ya tabbatar da harin mayakan, amma ya ce sojoji suna artabu da su.
- Matsalar Tsaro: Sabuwar barazana ta kunno kai a Najeriya —Magashi
- Yadda dakunan kwanan daliban jami’o’in gwamnati suka lalace
“Gaskiya ne ISWAP ta kai hari a garin Askira, majiya mai tushe ta tabbatar min cewa sojoji na gwabza fada da su, amma mutane sun tsere sun shiga dazuka,” inji shi.
Mayakan sun yi wa Askira/Uba dirar mikiya ne da misalin karfe bakwai an safiyar Asabar a cikin jerin gwanon motoci, suna luguden wuta ta yankin Ngude.
Injiniya Askira ya ce, “Mutanena sun shaida min cewa maharan sun shiga garin ne a cikin motoci 16 da aka girke bindigogi a cikinsu, lamarin da ya jefa daukacin garin cikin rudani. Addu’ata ita ce Allah Ya kare mutanen garin da sojoji.”
Wani jami’in tsaron sa-kai na Civilian JTF a garin, Yakubu Luka, ya ce mayakan sun kai farmaki a wani sansanin soji.
“Muna jira a kawo mana karin mutane daga garuruwan da ke kusa da mu, yanzu hakan rugugin harbi ne a ko’ina a garin.
“Muna kira da a turo jiragen yaki su taimaka wa dakarun da ke kasa, maharan sun fi mu yawa, motocin yaki biyar kawai gare mu,” inji Yakubu.