✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a Yobe

Wani bam da ake zargin ’yan Kungiyar Boko Haram sun dana ya hallaka mutum biyu tare da yi wa mutum uku mummunan rauni a kan…

Wani bam da ake zargin ’yan Kungiyar Boko Haram sun dana ya hallaka mutum biyu tare da yi wa mutum uku mummunan rauni a kan hanyar Damaturu zuwa Biyu a Jihar Yobe.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 4 da minti 45 na dare a jiya kusa da kauyen Azare.
Wani Dan Kato-da- Gora mai suna Madu ya fada wa Aminiya cewa wadanda lamarin ya rutsa da su fataken dabbobi ne da suke komawa Gombe bayan sun ci kasuwar Buni Yadi a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya bayyana cewa ’yan kasuwar sun hadu da ’yan Boko Haram inda nan take suka bude musu wuta.
“A kokarin tsira da rayukansu biyar daga cikinsu suka taka bama-baman da ’yan Boko Haram din suka binne inda nan take suka kashe mutum biyu daga cikinsu tare da raunata uku daga cikinsu. Da dama daga cikin ’yan kasuwar sun bata”. Inji shi.
Ya bayyana cewa harin shi ne irinsa na farko da ’yan kungiyar suka kai a yankin cikin shekara guda.
“Ban da wannan harin an shafe shekar guda ba a kai hari ba a yankin garin Gujba da Gulani”. Inji shi.