✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya tashi a kusa da barikin sojoji a Jalingo

Karo na uku ke nan a baya-bayan nan aka samu tashin bom a Jihar Taraba

Wani abu da ake kyautata zaton bom ne ya fashe a wani barikin sojoji da ke garin Jalingo, fadar Gwamnatin  Jihar Taraba.

Bom din ya fashe ne ranar Talata da dare kuma an ji kararsa a sassan garin na Jalingo.

Wasu, makwabtan barikin sojojin da wakilinmu ya zanta da su a safiyar Laraba na zargin a cikin barikin abin ya faru, wasu kuma na cewa a kofar shiga barikin ne.

A safiyar Laraba, wakilinmu ya ga an toshe hanyar shiga barikin, ana kuma umartar masu ababen hawa su sauya hanya.

Kawo yanzu dai babu wani rahoto a hukumance game da ko bom din ya jikkata wani, ko an samu asarar rai.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani game da lamarin daga kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, amma bai amsa kiran wayar ba.

Sau uku ke nan a baya-bayan nan aka samu tashin bom a Jihar Taraba, inda biyun farkon sun faru ne a Karamar Hukumar Ardo Kola, inda mutum sama da 30 suka rasu, wasu da dama kuma suka jikkata.

Kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai harin a wata masha a Karamar Hukumar Ardo Kola.