Wani bom ya raunata yara hudu masu shekaru shida zuwa 10 a garin Ngala da ke Jihar Borno.
A ranar Talata ce yaran suna wasa a wajen gidansu da ke Ngala, sai suka ga wani bakon abu da ake zargin bom ne da mayakan ’yan Boko Haram suka harba a lokacin da suke rike da garin a baya, amma bai fashe ba.
- Cocin Katolika ta karbi tuban Gwamnan Filato
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Mata A Zaben 2023
Daya daga cikin yaran da bom din ya raunata ya ce, “Ban san ko mene ne ba.”
Wani jami’in wata kungiyar agaji ya ce, “Yaran sun yi sha’awar sanin sa amma rashin dace da ban takaici da kuma ban mamaki ya zama nakiya da ba ta fashe ba; Kafin su ankara sai ya tashi.
“Fashewar wannan nakiya ta sa yaran suka samu munanan raunuka kuma nan take jirgin helikwafta na ICRC ya dauke su zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri.
“Yaran sun sami kulawa wajen ceton rai a asibiti, kuma suna kan matakin murmurewa yanzu,” in ji wani jami’in wata kungiyar agaji.
Ya ce, yin amfani da makamai masu fashewa a wuraren da jama’a ke da yawa na iya haifar da illar da ba ta dace ba kuma yana da babban hadari ga jama’a.
“Yara suna cikin hadarin mutuwa, rauni, raunin tunani da nakasa yayin da suke zaune kusa da bama-bamai da ba su kai ga fashewa ba.
“Har ila yau, yana da mahimmanci a tunatar da yara su guji daukar abubuwan da ba a san su ba, da kuma sanar da manya wadanda za su iya neman taimako daga shugabannin al’umma da hukumomi kan hakan.” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “A gaskiya yara da manya bai kamata su motsa abubuwan da ba a san su ba daga inda suka same su, kuma kada su bincika ko wasa da su.”