✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe sojoji 5, ya jikkata 15 a Borno

Hasfa daya da kanan sojoji biyar sun rasu, wasu 15 na asibiti a Chibok

Sojoji biyar sun rasu, wasu 15 kuma san raunuka bayan motocinsu sun taka bom din da mayakan Boko Haram suka dasa a Jihar Borno.

Sojojin, karkashin Birget na 28 sun gamu da ajalinsu ne a daura da kauyen Kwada Kwamtah Yahi a Karamar Hukumar Chibok da ke Kudancin Jihar ta Borno.

“Na ga yadda bom din ya yi wurgi da motar tana yawo a iska. Amma Mun kwashe gawarwakin mazajen da suka kwanta dama, cikinsu har da wani mai mukamin Laftanar da kuma kananan sojoji hudu.

“Akalla wasu sojoji 15 da samu raunuka kuma an kai su ana kula da su a Asibitin Birget na 28 na Rundunar Aiki da Cikawa a Chibok,” inji majiyarmu ta tsaro.

Da take tabbatar da harin, majiyar ta ce motocin sojojin da ke sintiri a yankin sun taka bom din da mayakan suka dasa ne a safiyar Alhamis, lamarin da kai ga dakarun sun kwanta dama.

“Abun takaici ne ya faru a Chibok inda motar Kwamandanmu na ayarin samar da tsaro ta taka bom ta kuma yi kaca-kaca gaba daya.

“Mun rasa zaratan sojoji amma hakan ba zai sanyaya mana gwiwa ba a aikinnmu na kawar da su [mayakan Boko Haram],” inji majiyar tsaron.

Wani babban jami’in dan banga da ke cikin tawagar aikin sintirin kakkabe mayakan Boko Haram daga kauyen Kwada Kwamtah Yahi a yankin Chibok, Yohanna Bitrus, ya tabbatar wa wakilinmu cewa motocin sintiri biyu na dakaru ne abun fashewar ya tashi da su.