✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe mutum 4, wasu 17 sun jikkata a Iraki

Harin bom ya kashe mutum hudu tare da jikkata wasu 17 a birnin birnin Sadr na kasar Iraki.

Wani harin bom ya hallaka mutum hudu tare da jikkata wasu 17 a birnin birnin Sadr da ke Baghdad, babban birnin kasar Iraki.

’Yan sanda da jami’an lafiya a birnin mai sun ce an kai harin ne a wata motar da aka ajiye a kasuwar kayan gwanjo a unguwar da ’yan Shi’a ke da rinjaye.

Harin na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan harin jirgi mara matuki da aka kai wa dakarun hadin gwiwar da Amurka ke jagoranta a Irbil da sansanin sojin Turkiya a Arewacin Iraki.