✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe Jagoran Civilian JTF, 5 sun jikkata a Borno

Sun taka bom ne a lokacin da suke gudanar da aiki a Karamar Hukumar Biu

Bom ya kashe wani jagoran jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF, wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka bayan sun taka bom a Jihar Borno.

Wani babban jami’in Civilian JTF, Mohammed Aliyu, ya ce kwamandan mai suna Ibrahim Maliya da abokan aikinsa sun taka nakiya ne a lokacin da suke gudanar da aiki a kauyen Maliya da ke gundumar Mandaragarau a Karamar Hukumar Biu ranar Laraba.

AFCON 2021: Za a kece raini tsakanin Abubakar da Salah a wasan Kamaru da Masar
Najeriya A Yau: Ma’anar hijabi a idon duniya
“Mun samu labarin rasuwar daya daga cikin zaratan ’yan Civilian JTF wanda ya kwanta dama a yau (Laraba) a bakin aiki, wanda hakan ya girgiza mu matuka. Allah jikan Miya da rahama, Ya kyautata makwancinsa.” inji Mohammed.

Ya bayyana cewa jagoran nasu da ya rasu, Ibrahim Maliya Saidu, jarumi ne wajen yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP a lokuta daban-daban, kuma shi ne Sakataren rundunarsu a Karamar Hukumar Biu.

Aminiya ta gano cewa mutum biyar din da suka samu raunkuna suna kwance a halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a wani asibitin da ake jinyar su a garin Biu.

Da yake ta’aziya, wani mai suna Junaid Jubril Maiva ya rubuta a Facebook cewa, “Innalillahi Wa Innah Ilaihil Raj’un, Allah Ya jikanka dan uwanna, Ibrahim Maliya Saidu Maliya.

“Ya taka bom din da Boko Haram ta dasa ne a Mandaragarau da ke Biu, tare da sauran abokanmu, ciki har da Dokta Suleiman Sykami. Sykami da sauransu da suka samu raunuka kuma suna samun sauki,” inji Maiva.