Tashin bom ya hallaka ‘gwamnan’ kungiyar Taliban a lardin Arewacin Faryab da ke kasar Afghanistan, Mawlawi Wakil Ahmad wanda aka fi sani da ‘Nazim’.
A ranar Asabar ce bom din ya Nazin tare da mayakan kungiyar guda bakwai kamar yadda kakakin ’yan sandan lardin, Abdul Karim Yurash ya tabbatar.
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
Ya ce gwamnan Taliban din da sauran mutum bakwan da sun mutu ne a lokacin wani bom din da suke dauke da shi ya fashe da misalin karfe 2 na dare a yankin Dawlat Abad.
Wasu da dama kuma sun samu raunuka samakamakon tashin bom din, duk da cewa ’yan Taliban da ke lardin na Faryab ba su ce komai game da lamarin ba tukuna.
Wani rahoto na kafar TOLO News kuma ya ce an kashe mayakan kungiyar Taliban guda hudu tare da kwamandansu a yankin Bati Kot da ke Lardin Nangarhar ranar Juma’a da dare.
Afghanistan na fama da hare-haren ta’addanci duk da kokarin samar da zaman lafiya da aka yi da kuma yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin kasar a birnin Doha na kasar Qatar, domin kawo karshen rikicin da ta shekara 20 tana fama da shi.