Wani bom da ’yan kungiyar a-waren Biyafara (IPOB) suka dasa ya tashi sa su tare da jikkata su.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce bom din ya tashi da ’yan ta’addan ne a kan titin Eke Ututu zuwa Orsu da ke Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo a ranar Laraba.
- Zulum, El-Rufai da Buni za su a jagoranci kwamitocin babban taron APC
- Jarumin fina-finan Nollywood, Jim Iyke, ya musulunta
Kakakin Rundunar Sojin Kasa Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ne ya sanar a Enugu a ranar Alhamis cewa bom din ya yi wa ’yan ta’addan munanan raunka.
“’Yan ta’addan sun taka abin fashewan da suka dasa ne a yayin da suke kokarin tserewa bayan sojoji sun kai samame a wasu hanyoyi a yankin Orlu, Karamar Hukumar Orsu.
“Haramtacciyar kungiyar ta sha dasa abubwan fashewa a kan hanyoyi da sojoji ke bi suna sintiri, da nufin cutar da sojoji amma ba su taba yin nasara ba.
“Muna rokon al’ummar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya masu son zaman lafiya da su sanar da sojoji kan wuraren da suke zargin akwai abubuwan fashewa domin su kwance su,” inji shi