Matashin dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen haifaffen Najeriya Boluwatife Balogun ya nuna sha’awar yi wa Najeriya kwallo a duk lokacin da aka gayyace shi. dan kwallon ya koka ne, bayan Hukumar NFF ta ki gayyatarsa don yi wa Najeriya kwallo a kowane mataki. Balogun ya shafe kimanin shekara biyu kenan yana kwallo a kulob din matasa na Barcelona da ke Sifen.
Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun nuna dan kwallon yana da takardar izinin zama dan kasa ga kasashe uku da hakan ya sa yake da zabin kasar da ya ga dama ya yi wa kwallo. Yana da takardar zama dan kasa ta Holland da ta Faransa da kuma Najeriya.
dan kimanin shekara 18 ya ce Hukumar NFF ta taba gayyatarsa sau daya don ya buga wa kungiuyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da U-17 wasa amma bai samu damar halarta ba saboda raunin da ya samu a wancan lokaci amma tun daga nan NFF ba ta sake gayyatar sa ba.