✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bollywood: Jarumin fina-finan Indiya Ramesh Deo ya rasu

Jarumi Ramesh Deo ya rasu sakamakon bugun zuciya yana da shekara 93 a duniya.

Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finai ta Bollywood ta kasar Indiya, Ramesh Deo, ya rasu a sakamakon bugun zuciya.

Dan jarumin ne ya sanar da mutuwarsa a daren ranar Laraba inda ya ce mahaifinsa ya rasu ne a ranar a asibitin Kokilaben Dhirubhai Ambani, yana da shekara 93 a duniya.

Ramesh ya fito a fina-finan Indiya sama da 250, ya kuma shafe wajen shekara 60 ana damawa da shi a masana’antar Bollywood.

Jarumin ya yi fice wajen taka rawa daban-daban a cikin fina-finai, tun daga kan likita, mugu, mahaifi da sauransu.

Wasu daga cikin fina-finansa da suka yi fice sun hada da Aarti, Anand, Aap Ki Kasam, Mere Apne, Jeevan Mrityu, Saraswatichandra, Teen Bahuraniyan, Khilona, Ghayal Once Again, Jolly LLB da sauransu.

Kazalika, Ramesh ya ci gaba da fitowa a fina-finai masu dogon zango na yankin Marathi da sauran shirye-shiryen gidajen talabijin.

An haifi Ramesh Deo ne a yankin Amravati Maharashtra, sannan ya fara fitowa a fina-finai a 1951 a cikin fim din Paatlaachi Por.

Ya rasu ya bar mata daya mai suna Seema Deo da kuma ’ya’ya biyu,wato Ajinkya Deo da kuma Abhinay Deo.