✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bola Tinubu: Wane ne sabon shugaban kasar Najeriya

Tarihi da gwagwarmayar Bola Ahmed Tinubu.

An fara wallafawa ranar 24 ga watan Fabrairu, 2023.

A safiyar ranar 1 ga watan Fabrairu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ya wayi a matsayin zababben shugaban kasar Njeriya.

Wata daya cur ke nan kafin 29 ga watan Maris, ranar bikin zagayowar murnar ranar haihuwar zababben Shugaban Kasa.

A karshen zai cika shekara 71 a duniya, sannan bayan wata biyu ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin Shugaban kasa a wannan karo na Jamhiriyyar Tarayyar Nijeriya a inuwar jam’iyyar APC.

Wannan shi ne abin da yake buri koyaushe. Ya kwashe kusan shekara 40 yana gina siyasarsa.

Siyasar Tinubu

Hakika Tinubu ya zama shugaba a baya. Wato Shugaban daliban Koyon Akanta na Jami’ar Jihar Chicago a Illinois ta kasar Amurka a1978. A nan ya fara dandana harkokin siyasa. Tun daga nan ne ya fara taku sannu a hankali a fagen siyasar Nijeriya.

Da farko ya lashe kujerar Sanata a Legas a 1993, sannan ya zama Gwamna a karkashin Jam’iyyar AD a 1999 bayan kwashe shekara hudu yana gudun hijira a waje.

Bayan shekara hudu ya tsira daga guguwar Jam’iyyar PDP da ta yi awon gaba da sauran gwamnonin Jam’iyyar AD a yankin Kudu masu Yamma. Daga nan ne ya kintsa wa sake gina jam’iyyar Yarbawa.

A lokacin zaben shekarar 2007 ya rigaya ya zama gagarabadau a yankin. Ya samu nasarar dora wanda ya gaje shi a kujerar Gwamnan Legas tare da taimaka wa sauran ’ya’yan jam’iyyar suka lashe kujerunsu a yankin.

Amma duk wanda ya san Tinubu, ya san burinsa ba ya tsaya ne a siyasar yanki ba. Shi ya sa da ya samu dama a shekarar 2015 ya yi hadakar da za ta kusanto da shi wajen cim ma burinsa, zama Shugaban kasa, sai ya rungume ta, ya mayar da kansa wani dan siyasa mai fada-a-ji a kasa.

Sai dai ba a ruwan sanyi hakan ta samu ba, sai da ya hada da sadaukarwa.

Jiga-jigan ’ya’yan jam’iyya sun tarwatsa yunkurinsa na zama mataimakin Buhari a lokacin, inda suka ce ’yan Najeriya ba za su amince da tikitin Musulmi da Musulmi ba.

Hakan ya sa Tinubu ya kawo wani ya maye shi, wato Yemi Osinbajo.

Yanzu da Buhari ke kan hanyar kare wa’adinsa Tinubu na da yakinin lokacinsa ne ya zo na ya shugabanci Najeriya, hakan ne ya sa ya samar da wata kalma da ta yi fice a fagen siyasa -‘emilokan  (yanzu lokacina ne).

Tinubu na iya kasancewa ya tsufa kuma yana da matsala a jiki kan lafiyarsa da furta kalmomi masu kurakurai a wajen kamfe, wanda hakan ke sa shakku kan karfin iya gudanar da mulki, amma zai zama kuskure a raina tsohon Gwamnan na Jihar Legas.

Tsayuwar dakan da ya yi har ya kada abokan hamayya a zaben fidda-gwanin dan takarar Shugaban kasa na watan Yunin 2022, ta isa zama manuniya kan gogewarsa a fagen siyasa.

Daidai ne in aka ce jiga-jigan jam’iyyar ciki har da Shugaba Buhari da Shugaban Jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ba su so Tinubu ya samu tikitin ba.

Mutum daya da zai iya taka masa birki shi ne Shugaban Kasa, amma tafiyar kaguwa da rashin yanke shawarar Buhari sun sa yunkurinsa na kawo abokinsa siyasarsa Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan ya gaza samuwa.

Tinubu ya hango hakan tun kafin ranar zaben fid-da-gwanin, don haka ya zo da makaman yaki — wasu za su ce makaman su ne kudi, abin da ake jin sabon tsarin kudi da ake yi yanzu an shirya shi ne don murkushe shi, kamar yadda magoya bayan Tinubu da wasu ’ya’yan APC suke zargi – sai dai zai kasance kuskure a mance kokarinsa na kulla kawance a sassan kasar nan.

Ga Tinubu wannan dama ce da ya kwashe sama da shekara 30 yana tattali kuma ba zai yarda wani abu ya rusa shi ba kuma a shirye yake ya ga damkar Shugaban kasa ko tsufa ko rashin lafiya ba su hana mutumin da ake masa lakabi da Zakin Bourdillon cim ma nasara ba.

Baswaja zuwa Amurka

Daf da zaben shekarar 2019 an ga manyan motocin daukar kudi guda biyu sun ratsa cikin mutane suka shige harabar gidan Bola Tinubu da ke Titin Bourdillon a Ikoyim Lagas. Bayan ficewarsu sun bar tambayoyi masu yawa.

Shin takardun zabe suka kai kamar yadda wasu ke zargi? Ko kuwa kudi suka kai kamar yadda wasu ke cewa domin a yi amfani da su wajen gudanar da zabe? Shin kudinku ne? Tinubu ya tambayi wasu ’yan jarida da suka tambayi me motocin daukar kudin suke yi a gidansa. “Me ya sa kuke shan Panadol kan ciwon kan wani?”

Abin fahimta, tun bayyanar Tinubu a harkokin kasa a 1991 wato tsawon shekara 40 yake ta tada hazo. Ana ci gaba da tambayoyi kan asalinsa. Babu bayanin kirki kan mahaifinsa, ba a ambatar sunansa, amma kowa ya san mahaifiyarsa. Ita ce Iyaloja (Shugabar ’Yan Kasuwar Legas, Hajiya Abibat Mogaji tun kafinma ta zama Iyaloja. Matar da take juya mata ’yan kasuwa (da maza) a Legas ita ta raini Tinubu da kanta.

Babu isassun bayanai kan kuruciyarsa. Babu bayani kan mahaifinsa – rasuwa ya yi ko rabuwa da mahaifiyar. Sai dai Tinubu ya sha yin magana kan kawunansa da ya ce sun taimaka wa rayuwarsa.

Ya ce a lokacin kuruciya shi mai kiriniya ne. Kuma yayin girma a Legas shi da abokansa suna bin motar mawaka Adeolu Akinsaya da Roy Chicago a yayin tafiya wajen kidi domin kurum su kalli wasansu a unguwanin Lagas.

Sai dai wata rana sun hau motar sai suka gan su a garin Ado- Ekiti inda dawowarsu Legas ta zama matsala saboda rashin kudi a hannunsu. Daga karshe sun samu dawowa bayan sun makale a bayan wata motar Koka Kola da ta nufi Legas.

“Na san na yi kiriniya kuma na sha duka,” in ji Tinubu a zantawarsa da ’an jarida lokacin da ya cika shekara 60 da haihuwa. Ya ce, “Eh, kwarai na yi kiriniya kamar shiga lambun mutane don tsinkar lemo duk da an gargade ni kan yin haka. Kuma nakan kashe kudin abincina a hayar keke.

“Nakan yi karya misali don karbar kudi daga kawunaina da sunan sayen littattafai biyar — Dic, Tion, Na, Ry — maimakon Dictionary wato kamus daya.

“Kuma littafi daya nake bukata. Na yi haka ne domin samun kudin da zan yi wasa ko hayar keke da sayen takalman wasa. Nakan je wasan kwallo a bakin ruwa, in dawo na yi dauda na gaji da yamma. Akwai kiriniyoyi masu yawa da na yi,” in ji shi.

Amma wasa a ruwa da shiga motocin mawaka, nan take ya yi watsi da su, a lokacin da ya kai shekara ashirin, sabon abu ne saurayi kamar Tinubu ya riga yawo a cikin motarsa kirar Baswaja da ya gada daga daya daga cikin kawunansa na wajen mahaifi.

Hakan ya faru ne a tsakiyar shekarun 1970. Me matashin zai yi da mota? Haka a lokacin ne rayuwarsa ta canza sosai.

Tinubu da abokansa sun taba zuwa biki a wani coci, da ya fita don sayo lemon kwalba a hanyarsu ta komawa wajen ’yar uwarsa da ke cocin sai ya ji wani sauti da ya canja rayuwarsa.

“An yi ruwan harsasai. Kuma ba don mun yi gudu zuwa cocin ba don ganin abin da ke faruwa a can, da na mutu. Harsashi ya samu matashin da ke tsaye tare da ni. Sai ya fadi ya mutu,” in ji shi.

Damuwa da abin da ya faru, sai mahaifiyar Tinubu ta ga akwai bukatar ta fitar da shi kasar waje tunda dama ya dade yana bukatar tafiya.

Kawunansa sun amince da shawarar sai ta sayar da gwalagwalanta ta kara da ’yar ajiyarta ta aika da shi waje. Shi kuma Tinubu ya sayar da motarsa ya kara da abin da mahaifiyarsa ta ba shi ya shiga jirgin japa, tun kafin a fara kiransa da wannan suna.

A Amurka ya zauna da danginsa sannan ya rika tafiye-tafiye a birane har sai da ’yan kudadensa suka kare. A Washington shi da wani abukinsa suka sayi wata mota mara rajista suna tasi da ita a filin jirgin sama. A Chicago ne rayuwarsa ta canza.

“Ina isa Chicago sai na wuce Kwalejin Richard Daley. Abin ban sha’awa ne sosai,” in ji shi.

Kudin da ya ajiye a sanadiyar tukin tasi a Washigton suna da dan dama.

“Da su na biya kudin hayar gida da na karatu a Jami’ar Chicago,” in ji shi.

Don samun karin kudin shiga sai ya rika aikin gadi a wani wajen aikin gini sannan ya yi aikin wanken kwanuka inda kullum ke cancada ado idan zai je aikin. daya daga cikin abokan yarantarsa a Legas, Tunde Badejo wanda suka hadu a Chicago ya tuna Tinubu a matsayin dan kwalisa. Badejo ne zai ba mu bayanin rayuwar dan siyasar mai dabara kan kwalliyarsa a lokacin yarinta.

“Kowace Lahadi Bola ba zai je ko’ina ba. Zai zauna a gida da abokansa. Za mu kawo lemukan sha. Amma babu abin da zai hana shi kallon talabijin. Yakan zauna a gaban talabijin yana kallon shirin siyasa musamman idan za a yi zabe sa Chicago, yana mayar da hankali sosai.

“Bayan gama kallon labaran siyasa, sai ya koma kallon kwallon Amurka (zari-ruga) wanda wasa ne na dabara. A lokacin Tinubu na digirinsa na farko ne a sashen harkokin kasuwanci (akanta da gudanarwa) a Jami’ar Chicago.

“Badejo a zantawar ya bayyana mamakinsa lokacin da ya samu labarin cewa Tinubu zai yi takarar shugaban daliban akanta a jami’ar.

Tinubu ya samu nasara daga nan ne aka kyankyashe dan siyasa mai dabara. Shiga hayaniya Ranar 10 ga Janairu 2022, a dakin ganawa da manema labarai da ke fadar Shugaban kasa a Abuja, Tinubu ya yi wani bayani da kowa ya san na zuwa tun shekara bakwai da sua gabata.

A wancan rana ya gana da Shugaba Buhari kuma ya shaida wa manema labarai cewa ya gaya wa Buhari burinsa na tsayawa takarar Shugaban kasa. Ba labari ba ne sai dai ranar ce karon farko da ya tabbatar a hukumanci.

An dade da tunanin Tinubu zai furta hakan. Yana son zama Shugaban kasa duk da cewa wannan ne karon farko da zai nema, amma bai taba boye cewa yana so ba.

Siyasar Tinubu ’yar lissafi ce da niyya kuma da gaske yake. Ta dogara ce da tuntubar abokan siyasa da kulla kawance da yarjejeniya da sauran ’yan siyasa.