Ta da kayar bayan da kungiyar Boko Haram ke yi ya rikide ya zama wata harkar kasuwanci ko masana’anta.
Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Ahmad Lawan, ya fadi hakan a zauren majalisar yayin da yake tsokaci a kan wani kudurin da aka gabatar ranar Alhamis.
“Yanzu dai Boko Haram ta zama wata masana’anta saboda abin da take yi ya yi hannun riga da addini.
“A cikin kungiyar akwai mabiya addinai daban-daban daga kasashe daban-daban”, inji shi.
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Borno
- Boko Haram ta sake kai hari a kauyen da ta kashe mutum 69
Kudurin dai na zuwa ne bayan da a makon nan kungiyar ta Boko Haram ta kai wasu hare-hare da suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 70 a wasu yankunan jihar Borno.
Sabbin hare-hare
Ranar Talata mayakan kungiyar suka kashe mutum 69 a kauyen Foduma Kolomaiya, mai tazarar kilomita 11 daga garin Gazaure na karamar hukumar Gubio.
Sannan ranar Laraba aka samu labarin cewa an kashe mutane biyar farar hula an kuma sace wasu mutum tara ranar Lahadi, lokacin da wasu da ake zargin ’yan Boko Haram din ne suka kai hari a kan wasu kauyuka uku, ciki har da Kondori, mai nisan kilomita shida daga Jakana a karamar hukumar Konduga.
Majalisar dai ta yanke kuduri cewa shugabanta da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila su gana da Shugaba Muhammadu Buhari su tattauna a kan karuwar hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan.