✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta saki bidiyon Daliban Kankara da ta yi garkuwa da su

An ga daya daga cikin daliban na rokon a rufe dukkannin makarantun boko

Kungiyar Boko Haram wacce Abubakar Shekau ke jagoranta ta saki wani sabon bidiyo da ke nuna daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina da aka yi garkuwa da su.

Sabon bidiyon da kungiyar ta saki a YouTube na nuna cewa yaran suna raye kuma kungiyar na kokarin samar da hanyar daidaitawa da gwamnati kan sakin su.

A cikin bidiyon mai tsawon minti shida da rabi, da kungiyar ta saki ranar Alhamis, an nuno Shekau yana bayani da daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da shi cikin jini.

Kazalika, an ga wasu daga cikin dalibai su 10 a bayan dalibin, dukkansu sun yi busu-busu jikinsu duk kura.

Wani daga cikin daliban da ya yi magana cikin harshen Hausa da turancin Ingilishi ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta daidaita da masu garkuwar, tare da gargadin ta kan kada ta yi amfani da karfin soji wajen kubutar da su.

Bidiyon dai ya nuna dalibin wanda ya yi magana a madadin sauran yana magana, yayin da sauran kuma ke tsaye a bayansa.

“Muna kira ga gwamnati da ta rushe duk wani rukunin masu aikin sa-kai na kato da gora, a rufe kowace irin makaranta sai dai ta Islamiyya.

“Muna kuma bukatar da a mayar da dukkan sojojin da aka turo nan saboda babu abin da za su iya yi musu wallahi. Jiragen nan ma a daina turowa. A taimaka mana daga halin da muke ciki,” inji dalibin.

Daga nan ne sai ’yan kungiyar suka hasko sauran daliban suna cewa bidiyon wani sako na zuwa ga Gwamnan jihar ta Katsina cewa daliban na cikin koshin lafiya.

Daliban dai sun rika yin kuka a ciki suna kira ga gwamnati kan ta taimaka ta duba halin da suke ciki domin ta kubutar da su.

A kwanakin baya ne dai wasu da ba a san ko su wane ne ba suka mamaye makarantar tare da sace daruruwan dalibai kafin daga baya kungiyar Boko Haram ta fito ta dauki alhakin sace su.