✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sake kwace garin Damasak

Kungiyar ta kafa tutarta bayan da ta kona ofisoshin ’yan sanda da masu ba da agaji a garin

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kwace iko da garin Damasak, hedikwatar Karamar Hukumar Mobbar ta Jihar Borno.

A yammacin Talata ne mayakan kungiyar suka kama garin, suka kafa tutarsu bayan da suka kona ofisoshin ’yan sanda da kungiyoyin agaji, makaranta, da kuma shaguna da gidaje.

Da yake tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Mobbar, Mustapha Bunu Kolo, ya ce, har yanzu maharan suna cikin garin, inda suke cin zarafin jama’ar da ba su ji basu gani ba, ba tare da an tunkare su ba.

Sai dai ya ce har zuwa yanzu bai samu bayanin adadin aka hallaka ba, kuma shi ba mazaunin garin ba ne.

Rahotanni daga Jihar Borno sun nuna tun a ranar Lahadi ’yan Boko Haram din suka fara afka wa garin, inda suka kashe soja uku da fararen hula 6.

Garin Damasak da ke kan iyakar Jamhuriyar Nijar ta yankin Arewacin Jihar Borno, nada nisan kilomita 180 daga Maiduguri, Babban Birnin Jihar.

Duk kokarin da Aminiya ta yi na jin ta bakin hukumomin tsaro, musamman sojoji, ya faskara har zuwa lokacin hada wannan rahoto.