Mazauna Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa, sun bukaci a samar musu da tsaro, bayan sace ‘yan mata da kungiyar Boko Haram ta yi.
Madagali na daya daga ciki kananan hukumomi da Boko Haram ta mamaye a 2014 kafin sojoji su kwato garin a 2015.
- Harin Boko Haram: Zulum ya koma Borno a jirgin yaki
- Boko Haram ta kashe mutum 7 a jajiberin Kirsimeti
- Boko Haram ta kaddamar da hari a kauyen Adamawa
- Boko Haram: An kashe sojoji 5, an sace fararen hula 35 a wani sabon hari
“An sace mana yaranmu, muna kiran gwamnati da jami’an tsaro da su taimaka su ceto mana su,” cewar iyayen yaran.
Mutanen yankin sun bayyana cewa wasu mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun sace ‘yan mata uku da matar aure yayin da suke aiki a gona a kauyen Dar a jihar.
Daga baya kuma ‘yan tada kayar bayan sun saki matar auren saboda tsufarta.
Wani mazaunin yankin, Iskarju Ezekiel, ya roki jami’an tsaro da su zakulo maboyar ‘yan tada kayar bayan a garin Madagali, wanda yake makwabtaka da Jihar Borno.
Mun yi kokarin jin ta bakin rundunar sojin ‘Aemoured’ da ke Yola kan lamarin, amma hakan ya faskara.