✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kona gidajen da aka gina wa ’yan gudun hijira a Borno

Mayakan Boko Haram sun cinna wa sabbin gidajen da aka gina domin sake tsuganar da yan gudun hijira a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar…

Mayakan Boko Haram sun kona sabbin gidajen da aka gina domin sake tsuganar da ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.

Mayakan sun kusta kauyen Gajibo da ke karamar hukumar ne suna harbi kan mai uwa da wabi sannan suka cinna wa sabbin gidaje 25 wuta.

A ranar Lahadi kuma mayakan kungiyar sun yi garkuwa da mutane 101 — kananan ’yan mata 53 da samari 48 — da suka je neman icen girki a kauyen Ngala.

Wani ganau, Modu Kundiri, wanda ke hanyar zuwa Maiduguri daga Gomboru, ya ce sojoji sun dakatar da motocinsu na kusan awa wuku a kauyen Logomani kafin daga bisani su bude hanya.

“Na ga akalla 25 daga cikin sabbin gidajen suna ci da wuta a kauyen Gajibo da ke yankin Dikwa,”in ji Modu.

Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, wanda ya tabbatar da harin na safiyar ranar Talata da kuma kona gidajen, ya ce maharan sun dasa abubwa fashewa a wurin da ake aikin ginin gidajen.

“Sojoji sun shaida mana cewa maharan sun dasa ababen fashewa a wurin, amma sojojin sun gano wasu bama-baman,” a garin na Gajibo mai nisan kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar.