✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kashe sojoji a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe soja hudu wasu kuma sun bace a wani kwanton bauna da kungiyar ta yi wa motocin sojoji da na fasinja…

Mayakan Boko Haram sun kashe soja hudu wasu kuma sun bace a wani kwanton bauna da kungiyar ta yi wa motocin sojoji da na fasinja a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno.

Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun bi sawun motocin ne a kusa da garin Mainok, suka bude musu wuta da tsakar rana inda suka kona motocin sojojin suka kuma saci makaman sojojin.

“Sun yi wa motocin sojoji kwanton bauna amma da rundunar kai dauki ta RRS ta kai agaji sai ta samu gawar soja hudu. Bayan bin sawu ne ’yan RRS suka gano bindigogin AK-47 akalla guda shida a dazukan da ke zagaye da wurin”, inji majiyar.

Wani shugbana ’yan sintiri kuma ya ce fararen hula da dama sun bace bayan harin a kauyen Kongiri kusa da Mainok a kan babbar hanyar zuwa Maidugu, jihar Borno.