✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kashe mutum 7 a jajibirin Kirsimeti

Mayakan Boko Haram sun kashe mutum bakwai tare da kona gidaje a kauyen.

Akalla mutum 7 ne suka mutu a wani hari da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kai kauyen Piyemi da ke kusa da garin Chibok a Jihar Borno.

Harin ya faru ne da misalin karfe 5 na Yammacin ranar Alhamis a kauyen Piyemi mai nisan kilomita 10 zuwa garin Chibok.

A cewar wani mazauni kuma dan kungiyar sa-kai kauyen mai suna Bitrus Yohaanna da ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin, wannan ba shi na farau ba domin maharan sun saba kawo musu farmaki a-kai-a-kai.

Bitrus ya ce a shekarar da ta gaba ma sai da mayakan na Boko Haram suka kai musu hari a irin wannan lokaci.

Ya ce a wanann karo sun kona gidade da coci guda biyu, sannan suka yi awon gaba da kayan abincin jama’a, daga nan kuma suka sake komawa cikin dajin Sambisa.

Wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce mutum shida suka mutu a harin ba bakwai ba.