✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kashe mutum 30 ta tashi sansanin soji a Borno

An kashe sojoji biyar da ’yan Civilian JFT 15 a harin na Ajiri.

Mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a kauyen Ajiri na Jihar Borno.

Maharan sun kuma tarwastsa wani sansanin soji da ke yankin na Karamar Hukumar Mafa a Jihar a harin Litinin.

“Mutane da dama sun rasu, cikinsu har da sojoji biyar, ’yan Civilian JFT 15 da karin wasu mutum 12,“ inji majiyarmu ta tsaro.

Ta bayyana cewa daruruwan maharan sun kutsa kauyen Ajiri ne a cikin motoci sama da 30 a daidai lokacin Sallar Asham, suna luguden wuta, lamarin da ya sa mutane tserewa zuwa cikin daji, har zuwa wayewar garin Talata.

Wani jami’in tsaron Civilian JTF, Bala Ibrahim, ya ce, “An gwabza kazamin fada na tsawon sa’o’i da ’yan Boko Haram din, daga karshe suka ci karfin sansanin sojan da ke Ajiri.”

Ya ce mayakan Boko Haram din sun kuma yi wagon gaba da wasu motoci biyar da kayan abinci daga kauyen.

Harin na Ajiri na zuwa ne kwana uku bayan wani makamancinsa inda aka kashe mutum 10 tare da kona gidaje a garin.