Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce, rikicin kungiyar Boko Haram ya yi ajalin mutum 100,000 tare da raba wasu sama da miliyan biyu da muhallansu.
Janar Irabor ya bayyana cewa dukiyar da ta’addancin Boko Haram ya salwantar a shekara 12 na rikicin, ta haura ta Naira tiriliyan 3.24 (Dala biliyan 9) a cikin shekaru 12.
- Kwanturolan Kwastam ya yanke jiki ya mutu a filin jirgi a Kano
- DAGA LARABA: Yadda aka zalunce mu a bainar jama’a, amma kowa ya kau da kai
Ya bayyana cewa ce abin da aka kashe wa Rundunar Tsaron Najeriya a shekara bakwai na Gwamnatin Buhari, bai kai kashi 35 cikin 100 na abin da sojoji suke bukata ba, kuma bai kai rabin kashi 1 cikin 100 na tattalin arzikin cikin gida ba.
A cewarsa, a shekara bakwai na muklin Buhari, kasafin da aka bai wa sojojin Najeriya tiriliyan N2.5 ne, kuma sun yi rawar gani wajen murkushe barazanar tsaro a cikin Najeriya.
Irabor ya yi wannan bayani ne a Taron Auna Ayyukan Ministoci na 2022 da aka kammala a Abuja ranar Talata.
A jawabin nasa, ya bayyana cewa duk da haka, a halin yanzu ta’addancin Boko Haram ya yi sauki, an ritsa ’yan ta’addar a wani dan tsukukun yanki.
Sai dai ya ce duk da haka wasun daga cikin sun sulale zuwa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda a halin yanzu suke addaba.