Hare haren ’yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya sun yi sanadiyyar mutuwar malaman makarantu dubu 2,295 tsakanin shekarar 2009 zuwa 2022.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata makala da Hukumar da ke Kula da Kwararrun Malaman Makarantu a Najeriya (TRCN) ta sanar a ranar Asabar.
Babban Magatakardar TRCN, Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye ne ya gabatar da wadannan alkaluma masu tayar da hankali lokacin da ya ke jawabi wajen taron kungiyar malaman makarantu na kasa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Ajiboye ya ce ayyukan ta’addanci sun tilasta rufe makarantu sama da 1,500, abin da ya haramta wa dalibai sama da dubu 600 zuwa karatu domin samun ilimi.
Jami’in ya roki gwamnatin Najeriya da ta sake fasalin tsaron kasar domin samar da tsaron da ake bukata wajen kare malamai da dalibansu a sassan kasar da ake fama da tashe tashen hankula.
Ajiboye ya ce a matakin farko, ya dace gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kuma tarayya da su gaggauta aiwatar da shirin kasa na samar da tsaro a makarantu ta hanyar ware wani kashe na kudin kasafinsu da zai kula da wannan bangare.