Ƙungiyar Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan takwararta na ISWAP da dama yayin wani ƙazamin rikici da suka tafka ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno.
Bayanai sun ce an kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 yayin harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ƙarƙashin jagorancin wani ta’adda mai suna Bakoura.
- Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal
- Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto
Wata majiya ta shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, cewa yaƙin da aka fara tun da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Fabrairu ya haɗa da sansanonin ISWAP da ke Toumbun Gini da Toumbun Ali.
Mayaƙan Boko Haram, waɗanda rahotanni suka ce sun ragargaji sansanin na ISWAP a wani ƙazamin faɗan ya ɗauki tsawon yini guda ana gwabzawa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe wasu manyan kwamandojin ISWAP musamman ‘yan kabilar Buduma a yayin harin.
A cewar majiyar, daga cikin ’yan ta’addan ISWAP da aka kashe sun haɗa da wasu manyan-manyan kwamandojin da ake kyautata zaton sun taka rawa wajen kisan kiyashin da aka yi wa manoma da dama a Kukawa a tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Janairu na wannan shekara ta 2025.
Majiyar ta ce mayakan Boko Haram sun yi wa kungiyar ta ISWAP asara mai yawa bayan da suka mamaye sansaninsu, inda suka ƙwace makamai da kayan aiki.
A wani yunƙuri na faɗaɗa hare-haren nasu, an ce mayaƙan na Boko Haram daga tsibirin Bokorram sun ɗaura ɗamara domin tunkarar mayaƙan ISWAP a Gemu da Mallam Karamti.
Zagazola ya bayyana cewa akwai yiwuwar ana gab da samun ƙarin fadace-fadace, musamman a Ƙaramar Hukumar Kukawa, yayin da mayaƙan Boko Haram ke ƙara ƙaimi wajen yaƙar ISWAP.