Mayakan Boko Haram sun yi dirar mikiya a yayin da ake shirin fara zabe a wasu rumfunan zabe a garin Goza da ke Karamar Hukumar Goza, Jihar Borno.
‘Yan bindigar sun kai harin tare da harba makamin roka ne ana cikin ake gudanar da zaben shugaban kasa da na ’yan Majalisar Tarayya a ranar Asabar.
Sarkin Goza, Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar harin inda ya ce, “Mayakan Boko Haram sun kai hari tsakiyar garin Goza tare da harbin bindiga.
“Mutum biyar sun ji rauni, kuma an kwashe su zuwa asibitin Maiduguri don yi musu magani.
“Da misalin karfe 8:30 na safe suka zo lokacin da masu zabe ke cikin layi suna jiran a tantance su.
“Mutane da daman da suka tsere sun ki dawowa, muna kokarin yadda za mu shawo kansu don su dawo,” in ji shi.
Ya ce jami’an tsaro sun hada kansu sun kori ’yan ta’addan.
“Hatta Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas na wurin, amma yanzu kura ta lafa,” in ji Basaraken.