Kungiyar Boko Haram ta sauya wa masanantar kera bom dinta matsuguni zuwa wasu dazuka da ke sassan Jihar Kaduna.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ce bangaren kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Bakoura Buduma ne ya sauya wa masana’antun bom din kungiyar matsuguni.
- Kwanan nan Najeriya za ta fara kera jiragen yaki marasa matuka —Minista
- Abin da ya haifar da juyin mulki a Sudan
PRNigeria ta ambato majiyoyin cikin gida a kungiyar na cewa an girke masana’antun bom din da kungiyar ke kira Amaliyyah ne a dazukan da ke yankunan Rijana, Igabi, da Chikun a Jihar Kaduna a matsayin maboya.
Majiyoyin sun kara da cewa hakan na faruwa ne a yayin da shugabancin kungiyar ISIS ke neman hadewa da rassanta a yankin Yammacin Afirka, wato ISWAP.
“Suna so su hade ne da ISWAP domin su kawar da bangaren Boko Haram din da Bakoura ke jagoranta,” inji wata majiya.
ISIS na shirin shigowa ne bisa umarnin shugabanta, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Quraishi, a yunkurinta na fadadawa da hade ayyukanta na ta’addanci.
Ana zargin hakan na da nasaba ne da kashe dimbin mayakan kungiyar da sojojin gwamnati suka yi a baya-bayan nan, a yankin Yammacin Afirka.
A ’yan makon jiya ne dai sojojin Najeriya suka sanar da kashe sabon shugaban kungiyar ISWAP, Malam Bako, watanni kadan bayan kashe shugabanta na farko, Abu Mus’aba Al-Barnawa.
Shi ma shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu, kuma tum bayan mutuwar shugabannin nasu, suke fama da rikicin shugabanci, a yayin da sojoji ke ci gaba da yi musu luguden wuta.
Akalla mayakan Boko Haram 5,000 tare da iyalansu ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, wanta kusan tun bayan mutuwarsa kungiyar ta karye.
A makonnin baya ma Shugaban Kasar Faransa, Emannuel Macron, ya sanar cewa sojojin kasarsa sun kashe shugaban kungiyar IS a kasar Mali.