Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne da safiyar ranar Laraba sun sake dawowa kauyen da suka kai wa hari a jihar Borno.
’Yan Boko Haram sun koma kauyen ne cikin kasa da awa 24 bayan sun hallaka mutum 69 kamar yadda rahotannin suka sanar.
Maharan dai sun afkawa kauyen Foduma (Felo) Kolomaiya, da ke karamar hukumar Gubio a Arewacin jihar maharan dai sun yi ta harbin jama’a tare da kone gidajen jama’a.
- Boko Haram ta kashe mutum 69 a Borno
- Boko Haram ta banka wa gari wuta a Borno
- Kwamandan Boko Haram ya mika wuya ga sojoji
A ranar Talata maharan sun kashe akalla fararen hula 69, yayin da wasu da yawa suka yi kaura daga gidajensu.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun dawo kauyen ne da misali karfe 6 na safiyar ranar Laraba.
“Mun yi ta samun kiran waya da safiyar Laraba cewa maharan sun dawo kauyen da suka kai harin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da yawa”, Inji shi.
Wata majiya daga ’yan bangar yankin sun ce, harin ya lakume rayuka yayin da wasu ke neman agaji.
“Jama’ar kauyen da aka kai wa harin sun ce a yanzu haka suna bukatar taimako. Wadanda aka kashe ’yan uwa sun binne su da safiyar Laraba, sannan suka sake dawowa kauyen da safiyar.
“Hakan ya sa jama’ar garin cikin fargaba sakamakon kashe kusan mutum 70 da kone gidaje”, kamar yadda wani dan banga ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho.