Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta ce ’yan kungiyar Boko Haram sun kashe dakarunta uku a garin Magumeri da ke Karamar Hukumar Borno.
Kanar Tomothy Antigha, Mataimakin Daraktan Sashen Yada Labarai na runduna ta takwas shi ne ya bayyana haka a sanrwar da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata a Maiduguri.