Aƙalla sojoji shida ne suka jikkata, yayin da Boko Haram suka kai musu hari da jirgi mara matuƙi, a yankin Wajiroko da ke Ƙaramar Hukumar Damboa a Jihar Borno.
Harin ya faru ne a daren ranar Kirsimeti, awanni kafin Shugaban Hafsan Sojin Najeriya ya isa Maiduguri, don gudanar da bikin tare da dakarun da ke bakin daga.
- Fashewar tukunyar gas yayi ajalin mutum 1, wasu sun jikkata a Neja
- An kai hari kan makiyaya an kashe shanu da dama a Filato
Wata majiyar soja, ta ce: “’Yan ta’addan sun zo da yawa suna harbe-harbe, amma mun yi amfani da makamanmu masu karfi muka kore su.
“Amma, abun takaici, wasu daga cikin sojojinmu sun jikkata yayin harin.”
Bayan haka, ’yan ta’addan sun tura jirage masu ɗauke da makamai da bama-bamai, wanda ya lalata kayan sojoji.
Majiyar ta ƙara da cewa, “An lalata wata motar sojoji guɗaya, an kuma kai sojojin da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.”