Hukumar Kawar da Ababen Fashewa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNMAS) da hadin gwiwar cibiyar samar da zaman lafiya da tallafi da kawayensu sun ce fararen hula 755 ne nakiyoyi suka kashe a Najeriya cikin shekaru shida da suka gabata.
- El-Rufai ya dawo da malaman firamare da ya kora a 2022
- Yadda aka yi jana’izar matar gwamnan Kano na farko Audu Bako
Kodineta na Kasa kan shirin kawar da nakiyoyi, Guruf Kyaftin Sadeeq Garba Shehu (murabus) ne ya sanar da haka a taron ranar wayar da kan jama’a kan illolin nakiyoyi da aka gudanar a Maiduguri.
Ya ce ko da yake an ci karfin matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najariya, har yanzu rayukan al’ummomin da ke komawa garuruwansu a yankin na fuskantar barazana saboda yaduwar abubuwan fashewa, lamarin da ke hana su ’yancinsu na walwala.
Bugu da kari, fargabar tana hana musu shiga cikin dazuka ballantana su noma gonakinsu, wanda hakan yake barazana ga samar da wadataccen abinci.
Ya kara da cewa, “a shekaru uku da suka gabata, Najeriya ce kasa ta biyu a duniya wajen yawan mutanen da aka kashe da hanyar kunar bakin wake, inda ’yan kunar bakin wake suka kashe mutum 619.
“Har yanzu akwai wuraren da abubuwan fashewa da aka jefa ba su fashe ba, wanda ke bukatar sai an share wuraren domin manoma su samu tabbaci da kwanciyar hankalin noma gonakinsu.”
Ya kuma yaba wa hukumomin kasashen duniya bisa irin taimakon da suke ba wa Najeriya wajen gane hakan ya samu.