Gwamnatin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da ’yan bindiga masu satar mutane da neman kudin fansa na aiki kafada da kafada a yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Ministan Watsa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka bayan taron Majalisar Zartarwa da shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa ranar Laraba a Abuja.
- APC ce ta shirya shirme da sunan sakamakon zaben kananan hukumomin Katsina – PDP
- Hadarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum 26 a Sakkwato
Ya ce abin da ke faruwa a yanzu akwai kawance tsakanin ’yan bindiga da Boko Haram, bayan an tambaye shi ya fadi wadanda suka kai hari a Jihar Filato.
Ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar kan harin jirgin kasa da aka kai a Kaduna ya nuna “akwai alaka tsakanin ’yan bindiga da mayakan Boko Haram da ke yankin Arewa maso gabashi.
“Ina mai tabbatar muku da cewa akwai kawance tsakanin ’yan bindiga masu satar mutane a yankin Arewa maso Yammaci da kuma mayakan Boko Haram da ke Arewa maso Gabas.
“Sai dai kuma babu shakka duk wani ta’addanci bai fi karfin gwamnati ba kuma za mu ci gaba da tunkarar lamarin.”
A nasa jawabin, Ministan Tsaro Bashir Saleh Magashi, ya ce hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu wajen gano wadanda ke da hannu a wadannan hare-hare, “kuma nan ba da jimawa ba za mu sanar da ku masu duk wasu masu hannu a ciki.”