Kungiyar Boko Haram, ta yi ikiraren cewa mayakanta ne suka yi garkuwa da daliban makarantar GSSS Kankara, Jihar Katsina.
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon sauti inda ya yi ikirarin cewa kungiyar ta dauke yaran ne da nufin ‘kare Musulunci da kuma yakar kafirci’.
- GSSS Kankara: ’Yan bindiga sun tuntubi Gwamnatin Katsina
- An gano inda daliban Makarantar Kankara suke —Masari
“A takaice kawai, wannan aiki da ’yan uwa suka gabatar a cikin garin Katsina, mu ne muka yi. Mai magana Abubakar Shekau, Shugaban Jama’atu Ahlis Sunnah Lidda’awati Wal Jihad [Boko Haram]”, inji shi.
Tun da farko, Shekau ya riya cewa: “Wannan aiki da ya faru a Katsina, don addini ya daukaka, kafirci ya yi kasa ne muka yi wannan aiki…
“Karatun boko ba karatun Allah da Annabi ba ne ba kuma abin Allah da Annabi ake koyarwa a ciki ba.
“Sai dai ma addinin Musulunci ne ake rusarwa a ciki. Ko da an boye, Allah Mai sama, Mai Kasa Ya sani”, inji Shekau.
Ikirarin Boko Haram na garkuwa da daliban na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara sun tuntube su.
Masari wanda ke bayani ga Shugaba Muhammadu Buhari game da halin da ake ciki kan daliban ya ce an fara tattaunawa da maharan kan sako daliban.
“Gwamnan ya ce masu garkuwa da daliban sun tuntube su kuma ana magana da su kan dawo da yaran cikin koshin lafiya.
“Masari ya kuma tabbatar da wa Shugaba Buhari da cewa hukumomin tsaro sun gano inda aka kai daliban”, inji sanarwar da kakakin Shugaba Kasa, Garba Shehu, ya fitar bayan ziyarar ga Shugaba Buhari, wanda ya ke hutu a mahaifarsa, Daura da ke jihar, ranar Litinin.
A ranar Juma’a da dare ne dai ’yan bindiga suka far wa makarantar kwanar ta GSSS Kankara suka inda suka yi musayar wuta da jami’an ’yan sanda kafin su yi awon gaba da dalibai zuwa cikin daji.
Zuwa yanzu dai ana ta samun bayanai masu karo da juna game da hakikanin daliban da aka yi garkuwa da su a harin.