✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram: An kashe sojoji 5, an sace fararen hula 35 a wani sabon hari

An kai wa tawagar sojojin hari ne ranar Asabar a jihar Borno.

Sojoji biyar ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu ’yan bindiga da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka yi wa tawagar sojojin kwanton bauna a ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, maharani sun kuma yi garkuwa da wasu fararen hula 35 a wani harin na daban da suka kai a ranar Lahadi.

An kai wa tawagar sojojin hari ne ranar Asabar a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwana daya da aukuwar hari ne, masu tayar da kayar bayan suka far wa ayarin wasu motoci inda suka yi garkuwa da fasinjoji 35 tare da kashe wata mata kamar yadda rahoton na AFP ya tabbatar.

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kasha fiye da mutum 30,000 tun bayan da ta daura damarar ta’ddanci a shekarar 2009, inda a bana kadai ta kai munanan hare-hare akalla 11 a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

A ranar 28 ga watan Nuwamban 2020 ne mayakan Boko Haram suka yi wa wasu manoman shinkafa fiye da 100 yankan rago a garin Zabarmari da ke jihar Borno.

Kazalika, a makon jiya ne shugaban wani bangare na kungiyar, Abubakar Shekau, ya yi ikirarin sace fiye da dalibai 300 na makarantar sakandiren kimiyya da ke garin Kankara a jihar Katsina.