Wani boka da ke shirya wa ’yan ta’adda maganin bindiga a Jihar Katsina, ya fada a komar ’yan sanda.
Baya ga shirya hada bindigar, bokan kan yi wa ’yan ta’addan addu’ar kariya don kada a kama su.
- An kwace bindigogi 5 a hannun wadanda ake zargi da kai hare-hare a Osun
- Abba Gida-gida ya yi barazanar kauwarace wa yarjejeniyar zaman lafiya a Kano
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya shida wa manema labarai ranar Talata a Katsina cewa bokan da aka cafke na zaune ne a yankin Karamar Hukumar Sabuwa ta jihar.
Ya kara da cewa, sun samu nasarar damke shi ne sakamakon bayanan sirri da suka samu a kansa.
A cewarsa, bokan na shirya maganin ne kan N60,000 don amfanin ’yan fashin daji da sauran gaggan masu laifi a jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara.
Isah ya ce bokan ya amsa laifin da ake tuhumar sa, tare da cewa za su gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.
(NAN)