✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bello Turji na neman miƙa wuya ga sojoji —Janar Musa

Janar Christopher Musa ya ce bayan halaka mataimakin Bello Turji da wasu manyan kwamandojinsa da sojoji suka, dan ta’addan ya far neman yadda zai miƙa…

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji na neman ya miƙa wuya bayan ragargazar da sojoji suka tsananta a wuraren da yake addabar mutane.

Janar Christopher Musa ya ce bayan halaka mataimakin Bello Turji da wasu manyan kwamandojinsa da sojoji suka, dan ta’addan ya far neman yadda zai miƙa kansa.

“Mun riga mun kawar da mataimakinsa da wasu manyan mataimakansa, dole ta sa ya sako mutanen da ya yi garkuwa da su s ke hannunsa.

“Ina tabbatar maka cewa yanzu haka ya fara maganar cewa shi babu abin da yake so, a shirye yake ya mika wuya,” a cewar Christopher Musa a yayin hirar da aka shi da shi a tashar talabijin ta Channels a ranar Juma’a.

Duk da haka ya jaddada muhimmancin yi adalci da kuma hukunta duk masu hannu wajen salwantar rayukan al’umma.

Ya bayyana matsalar da suke samu wajen Bin sawu da halaka Tirji ita ce ta samun bayanai a kan lokaci, saboda dan ta’addan ba shi da tabbas a yanayin motsinsa.

Ya ce, “yana shiga cikin al’umma kuma mutane sun san shi sai sai matsalar kafin su ba mu bayanan sai an yi kamar awa biyu, kuma a lokacin ya riga ya bar wurin.

“Saboda haka kafin mu je ya riga ya yi daɗe da tafiya ya bar wurin,” in ji shi.