Dakarun Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar JTF na Operation Hadin Kai, sun kai farmaki dajin Sambisa, inda suka ƙwato makamai da alburusai masu yawa.
Wata majiya ta bayyana cewa sojojin, sun kai samame yankin Ukuba tare da bataliya ta musamman ta 199 da kuma ‘yan sandan JTF domin bincike da ƙwato makaman da ‘yan ta’adda suka ɓoye.
- Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo
- Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
Da suka isa wajen da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 1 ga watan Maris, sun tarar da cewa ‘yan ta’addan sun tsere, inda suka bar makamai da kayan yaƙi da dama, ciki har da injina daban-daban, bindigogi, bututun RPG, da wasu kayayyakin fashewa.
Sojoji sun ce wannan farmakin yana daga cikin matakan da suke ɗauka domin fatattakar ragowar ‘yan ta’adda daga dajin Sambisa da kuma ƙwato makaman da suka ɓoye a yankin.