Wani fitaccen boka da ake kira Akwa Okuko Tiwara Aki a Jihar Anambra, ya bayyana dalilan da suka sa ya kasa ɓacewa a lokacin da masu garkuwa da mutane suka kai masa farmaki, abin da ya kai ga fadawa komarsu.
Bokan wanda aka fi sani da suna Oba ya ce, ya ki bacewa ne domin kauce wa asarar rayukan da ke iya biyo baya sakamakon harin.
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice biyu a Sakkwato
- AU ta bai wa sojoji wa’adin dawo da tsarin mulki a Nijar
A kwanan nan ne batun sace bokan ya karade shafukan sada zumunta lokacin da ta fada komar masu garkuwa da mutane a lokacin da yake shakatawa da wasu abokansa.
Aminiya ta ruwaito Oba na cewa wani abokinsa ya gayyace shi zuwa wani otel da ya mallaka, inda ya shaida masa cewar tuni har sun kashe naira dubu 300 a hutawar da suke yi, abin da ya sa shi kama hanya zuwa wurin.
Bokan ya ce, yana isa otel din sai ya ji karar harbin bindiga, yayin da ’yan bindigar suka kai masa hari, amma harbin ya ki ratsa shi, sai dai masu tsaron lafiyarsa guda biyu sun sheka lahira sakamakon harbin.
Oba ya ce, nan take masu garkuwa da mutanen suka tasa keyarsa zuwa cikin motarsu, inda suka gudu da shi, saboda ganin yadda ya ki tirjiya domin kauce wa rasa dimbin rayuka.
Bokan ya ce yana da hurumin bata domin kare lafiyarsa, amma yin hakan zai haifar da rasa dimbin rayuka, saboda haka ya gwammace ya mika kansa.
Oba ya ce lokacin da ake garkuwa da shi yana jin mutane suna cewa saboda bashin da ake binsa aka yi garkuwa da shi, amma wannan ba gaskiya ba ne.
Bokan ya ce masu garkuwa da mutanen sun shaida masa dalilin da ya sa suka je otel dinsa, domin gudanar da wani aiki, amma ba domin kai masa hari ba.