✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AU ta bai wa sojoji wa’adin dawo da tsarin mulki a Nijar

Amurka za ta ci gaba da bai wa Mohamed Bazoum taimako marar iyaka.

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta umarci sojojin Nijar su “koma bariki kuma su dawo da gwamnatin tsarin mulki” nan da kwana 15.

Wannan kashedi na zuwa ne kwanaki kadan bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasar da ke Yammacin Afirka.

Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya na Tarayyar Afirka ya “bukaci jami’an soji su yi gaggawar komawa bariki ba tare da wani sharadi ba sannan su dawo da gwamnatin tsarin mulki nan da kwana 15,” a cewar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.

Sojojin suna tsare da Shugaba Mohamed Bazoum a gidansa da ke fadar shugaban kasa tun ranar Laraba sannan suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatinsa.

Sai dai Janar Abdourahamane Tchiani da ya jagoranci juyin mulki a kasar ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa sannan ya yi gargadin cewa za a zubar da jini idan wata kasar waje ta tsoma baki a sha’anin cikin gida na Nijar.

Kasashen duniya dai na ci gaba da matsa lamba ga sojoji don su dawo da tafarkin dimokuradiyya.

Ranar Asabar Tarayyar Turai (EU) ta ce ba za ta amince da sojojin ba sannan ta dakatar da tallafin da take bai wa kasar nan take.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya ce kasarsa za ta bai wa Mohamed Bazoum taimako ‘mara iyaka’ sannan ya “jaddada muhimmancin ci gaba da mulkinsa” a kasar.

Mista Blinken ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da Mohamed Bazoum, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ranar Juma’a.

“Ya jinjina wa Bazoum a kan rawar da ya taka wajen tabbatar da tsaro a Nijar da kuma yankin Yammacin Afirka,” in ji sanarwar da kakakin Ma’aikatar Wajen Amurka Matthew Miller ya fitar.