An kama wani boka kan sace wata motar ɗaukar kaya mallakin wani kamfani a Jihar Bibuwai.
Noman ya shiga hannu ne tare da wani direba a kamfanin gine-gine na CHEC da ke aikin gyaran tituna a jihar.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Bibuwai, Catherine Aneneh ta ce a ranar Asabar suka samu rahoton cewa direban ya yi awon gaba da morar da aka tura shi ya kai duwatsu daga Ƙaramar Hukumar Ohimini LGA zuwa yankin Mase da ke Ƙaramar Hukumar ta Gabas inda ake aikin gyaran titi.
Ta ce daga bisani aka direban da bokan bayan an sami motar hannunsu a yankin Ikyurav da ke Ƙaramar Hukumar Kwande.
- Najeriya ta ba ƙasashen waje lantarkin N181.6bn a wata 9
- Dalilin da yunwa ta yi katutu a Arewa —Gwamnati
Catherine Aneneh ta bayyana cewa direban ya kasa bayar da cikakken bayani kan dalilinsa na kai motar wurin bokan, kuma ya kashe wayarsa tsawon kwana huɗu da ake nemansa.