’Yan sanda a Jihar Enugu sun damke wani boka da ake zargi ya harbe wani da ya nemi maganin bindiga a wurinsa a yankin Karamar Hukumar Isi-Uzo.
Aminiya ta samu rahoton cewa, bokan ya harbe mutumin har lahira a lokacin da yake kokarin jarraba ingancin maganin bindigar da ya hada masa.
- An yi zanga-zanga kan hana Adaidaita Sahu bin wasu titunan Kano
- Najeriya ba ta yin abin da ya dace wajen rage yawan haihuwa – Hukumar Kidaya
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Talata cewa, bokan ne ya kera bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe mutumin.
Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna bokan ya amsa cewa lallai ya yi amfani da bindiga kirar gida wajen harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutumin a inda yake sana’arsa ta tsubbace-tsubbace.
Bokan ya ce hakan ya faru ne lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada wa marigayin.
Ndukwe ya ce batun na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar inda ake ci gaba da bincike.