Sakataren Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken ya fara ziyarar kasashen Yammacin Afrika da Sahel.
Ziyarar na da nufin bunkasa kawancen Amurka da nahiyar musamman yankin Sahel a fanni tsaro da tabbatuwar dimokuradiyya.
Ziyarar wadda Blinken zai shafe mako guda yana yi, zai fara ne da Cape Verde gabanin yada zango a kasashen Ivory Coast da Najeriya da kuma Angola.
Wannan ziyara dai, ita ce ta baya-bayan nan da sakataren wajen na Amurka ke kai wa ketare wadda ba ta shafi yakin Isra’ila a Gaza ko kuma yakin Rasha a Ukraine ba.
Kazalika, ziyarar na zuwa a daidai lokacin da ake samun rabuwar kai tsakanin kasashen Afrika game da yadda Amurka ke tunkarar yakin Isra’ila da Hamas da kuma yakin Rasha da Ukraine.
Ziyarar na matsayin biyan bashi kan alkawarin Joe Biden, na ziyartar Afrika cikin 2023, wanda ake ganin Blinken zai yi amfani da damar wajen karfafa alakar kasar da nahiyar.
Ziyara ta karshe da Blinken ya kawo Afrika ita ce cikin watan Maris din 2023, lokacin da ya yada zango a Nijar.
A wancan lokaci, ya ziyarci Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar, wanda bayan wata hudu da ziyarar sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin Bazoum.