✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya Biya N6.3m Kudin Kama Hayar Kabari

A masallacin da muka yi Sallah akwai takardun cikewa da masallata ke karba domin bayar da tallafin sayen filin kabari da jana'iza

Na zaune bai ga gari ba.

Abubuwan ban mamakin da dama na yi kicibis da su a tafiye-tafiyen da nake yi sun hada da talllace-tallace da a ka haska a gidajen talabijin a wata kasa a kan hanyoyin da mai rai zai iya bi ya saka jari ko adashen gata da ma tsare-tsaren asusun tanadi domin sayen kabari da jana’iza.

An fayyace damar da mutum yake da ita na ya yi wa kansa ko a yi masa ko ya yi wa wani makusanci irin wannan tanadi domin samun “jana’iza” ta mutuntawa bayan rai ya yi halinsa.

A yau na sami labarin cewa a wata kasa wani ya biya kudin da kimarsu ta kai sama da Naira miliyan shida da dubu dari uku (N6,300,000) domin sayen filin kabari da jana’izar iyayensa (uwa da uba) da shi kansa idan ajali ya zo.

Wadannan makudan kudaden za su iya sayen filin kabarin da za a bizne mamaci ne na tsawon shekaru goma kacal.

Bayan shekaru goma za a yi amfani da filin a saka wani ko wasu.

Domin kauce wa biyan kudi masu yawa, kicibis, a jumlace kuma kai tsaye, domin sayen filin kabari na wani takaitaccen lokaci kuma a dai-dai lokacin da mutum ke jimamin rasuwar nakusanci, a wata kasar da na kai ziyara a bara Musulmai sun fito da wani tsari.

A masallacin da muka yi Sallah akwai takardun cikewa (forms) da masallata ke karba domin bayar da tallafin sayen filin kabari da jana’iza.

A kowane wata an saukaka za a biya kimanin kudin Najeriya kusan dubu tamanin (N80,000).

Duk wanda ya bayar da kudin, to ya saya wa kansa da iyalansa kabari ke nan.

Bayan rayuwa za a kai shi da iyalansa su kwanta-dama cikin mutuntawa.

Kuma ba za a fitar da mutum ba bayan shekaru. Domin kudaden da ake tarawa a masallacin za a cigaba da biyawa duk wanda ya ke cikin makabartar kudin hayar zama cikin kabari.

Akwai al’ummar da suka inganta wannan harkar ta sana’ar filayen kabari.

Mutum zai shiga intanet ya zabi makabartar da ta kwanta masa da kuma irin kabarin da yake so, kamar misalin mai sayen tikicin shiga jirgi; ya zabi kujerar da ya ke so ya zauna.

Ikon Allah a irin inda ake samun garabasa, makabarta kyauta, da a ce za a rika biyan kudin filin kabari, ko hayar zama cikin kabi, ka na ganin mamata za su sami a saya masu makwanci?

Jumu’a 28 Rajab 1445

(9 Fabrairu, 2024)